BANIDA MADADIN KI A ZUCIYATA

 Banida madadinki a zuciyata masoyiya 

________________________________


Kinada kima A idanuna shiyasa bana iya dadewa ina kallon tsakiyar Idanuwanki.


Chikakkiyar gaisuwa, tareda budewar dukkan wasu kofofin farin ciki zuwa
gareki Abar kwatancena.


Idan gaisuwa ta kammala sai na wuce zuwa aiken da zuciyata tayi min mai dauke da sakonnin Qaunarki


Ya zama Dole Insamu Nutsuwa, Domin In Gabatar Da Natsattsen Sakona Zuwa Gareki Ma'abociyar Nutsuwa Da Fahimta


Dukkan wasu lafuzzan kaunata ina gabatar dasu agareki domin kece kikai awon gaba da Tunanina


Burin Zuciyata ki zauna cikin Qoshin lafiya ki taka lafiya ki sauQa lafiya kija ragamar mulkin zuciyata cikin koshin Lafiya Da Shauki.

Kece Kika Zamo Silar Tsamoni Daga Fadawa Cikin Ambaliyar Rudewar Rashin Tabbacin Zaman Lafiyar Zuciyata

Ina kara sanar dake cewa kece kadai na mikawa dukkan zuciyata domin ki shayar da ita madarar Zumar_Kaunarki

Na Sadaukar Miki Da Duk Farin Cikina. Fatana Akoda Yaushe Ki Kasance Acikin Yanayi Mai Dadin Dake Dadada Ruhi.

Post a Comment

0 Comments