Kayatattun wasikun masoya masu dadi da sanyaya zuciya 2023
Assalamu'alaiki Yakike hubbyn Sona da fatan kin tashi lafiya. Ina Fata Zaki Kasance Cikin Irin Matan nan Da Suke da Rabo a Duniya, Wa'yanda Suke Karban Masoyansu Hannu Biyu. Kada Ki Taba Cewa Masoyin Bakya Son Shi, Domin Hakan Yakan Janyo Rugewar Zuciyarshi a Tare Da Burin Shi. Nayi Tafiya Mai Tsawo Dayawa dan Ganin Murmushinki, Na Manta da Matsayi na domin Nuna Qauna Agareki. Na Qanqantar da Kaina Domin ki Yarda Dani. Na Shiga Hali na Kadaici a Da, Samunki Babban Nasara Ce cikin Rayuwata. Amincewarki Nake Nema domin Rubuta Labarin Soyayyarmu Jikin Bango Mafi Girman Daraja ajikin Dutsen da Masoya Suka Kasa Isa. Bawai Iya Kalliyarki Ce Ta Jawo ni Wurin ki Ba, Ba Iya Tafiya Ba, Ba Iya Zance Ba, Ba Iya Kallo ba, Ba Kyawawan Idanu Ba, Ba Kyakkyawan Fuska Ba, Ka Kyakkyawan Surar Jiki Ba, Sai Dan Allah Nake Qaunar Ki.
0 Comments