Yadda ake rubuta wasiƙun soyayya masu daɗi
Zan Fi Kowa Dacewa Idan Kika Rike Kaunar Da Ke Tsakaninmu Nai Maki Wani Tanadi Duk Sanda Kika Kasance Uwar ‘Ya’yan Mu Zuciyata Za Ta Kasance Mai Yabonki Da Kuma Nuna Maki Kulawa Wanda Uwa Take Bawa Danta, Ki Kasance Tawa Ta Har Abada. Idan Kowa Haka Ta Samu A Tsakaninmu Ba Abin Da Za Mu Nema A Cikin Wnnan Duniyar Saboda Ya Cika Mana Burin Mu Sai Dai Fatan Mugama Da Dunia Lafiya
02
Inuwarki Zata Min Dadi Farinkiciki Ki Zai Kayatar Dani, Rayuwarki Zata Amfanar Dani. Xuciyar Ki Zata Mini Rana, Kalaman Ki Zasu Min Magani, Tafiyarki Zata Debe Min Kewa, Murmushin Ki Zai Sani Farin Ciki. Ina Son Abunda Kike So Bana Qaunar Abunda Bakya So, Ina Son Me Sonki Amma Bada Soyayya Ba, Ina Kishi Akanki Sosai Bana Son Koda Quda Ya Taba Ki Bada Hakki Ba, Ko Kallon Banza Banso Naji Za’a Miki Bale Ma A Miki, Rayuwata Zata Cika In Dake. Ina Qaunar Ki.
03
Zan Kasance Da Kullum Da Handkerchief Akoda Yafe Ina Yawo Dashi Dauke Da Tambarin Soyayyar Ki, Domin Kada Kiyi Kuka Na Kasa Share Miki Hawaye, Ina Qaunar Smile A Face Dinki Koda Tuntube Kikai To Lallai Raina Zai Ciwo, A Karkashin Mulkina Kina Da Duk Wani Jindadi Da Mace Take Nema A Wurin Miji.
04
Aminci Da Yarda Ya Qara Tabbata Ga Mamallakiyar Zuciyata, Farin Wata Mai Haskaka Zuciyata, Kece Kika Zamo Farin Cikin Rayuwata, Ina Da Tabbacin Cewa Zuciyarki Tana Cike Da So Na Da Shauk’ina Had’i Da Bege Na Acikin Wannan Sansanyar Safiyar Kamar Yanda Tawa Ta Kasance Haka, Zai Zama Abin Alfaharina Cewa Wannan Sak’on Nawa Shine Abu Mafi Soyuwa Daya Fara Riskarki Cikin Wannan Ni’imtacciyar Safiyar Masoyiyata, Aminiyata Abokiyata. Shalele Na.
05
Godiyta Tayi Alkawarin Riskar Ki A Kowani Lokaci. Domin Nuna Karramawa Agareki, Rarrashina Zai Kasnce Dake Aduk Lokacin Da Kike Tare Dani. Lafiyata Itace Samun Naki Lafiyar, Idan Nai Farin Ciki Murmushinki Na Hango.
06
A Duk Inda Kika Je Ki Tabbatar Da Cewa Ina Biye Da Ke, Ko Da Ban Zo A Zahiri Ba To Kuwa Zan Zo Miki A Cikin Bacci, Ke Ma Za Ki Bayyana A Cikin Mafarki Na, Mu Kasance A Tare Da Juna, Cikin Wani Lambu Mai Cike Da Furanni Mabambanta Launi. Begenki Shi Ne Abun Yina A Kullum.
07
Lallai Ke Din Ta Daban Ce, Kina Da Wata Baiwa Wadda Ba Kowa Ne Zai Gane Hakan Ba, Daga Ciki Akwai Ta Zazzakar Murya Da Tattausan Murmushi. A Lokuta Da Yawa, Kalmomi Sukan Gagari Furtawa, Domin Bayyanar Miki Da Adadin Yadda Sonki Yake Kara Mamaye Zuciya Ta A Kullum. Bana Fatan Zuwan Ranar Da Zan Gaza Wajen Nemo Kalmomin Da Zan Furta Miki Cewa INA SON KI. Ganin Yau Ya Sani Fari Ciki Sosai I Love You
08
Daya Daga Cikin Abun Dake Zuciyata Shine Tinanin Ki, Tinanin Ki Ya Min Sarqa Ya Zarge Ni Nishi Nake Amma Dakyar Nake Numfashi. Na Biyu Shine Qaunar Ki, Qaunar Ki Tazo Tana Hiranta Min Cewa Idan Har Na Kuskura Na Rasaki Amatsayin Mata To Zata Iya Yin Ajalina Dakyar Na Bata Hakuri Nace Mata Ina Qaunar Ki.
0 Comments