Qayatattun Wasikun Soyayya Kenan.
09

Alkawari Ne Na Dauka, Ba Zan Taba Barin Damuwa Ta Wanzu A Cikin Zuciyar Ki Ba Matukar Muna A Tare Da Juna, Ina Fatan Nan Da Wani Dan Lokaci Ki Tabbatar Da Hakan Bayan Kin Zamo Mata A Gare Ni, Ke Kadai Zuciyata Ta Amincewa, Ki Huta Lafiya. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son Ki.

10

A Cikin Dukkan Mafarkan Da Nake Yi Bayan Haduwata Da Ke, Ban Taba Ganin Wata Rana Da Ta Zo Ta Kuma Wuce Ba Tare Da Na Gammu Tare A Cikin Lambu Mai Sanyaya Zuciyar Masoya Ba, Rayuwa Ce Mai Dadi Ke Gudana A Tsakanin Mu, Ina Fatan Wannan Rana Ta Bayyana A Gare Ni A Zahiri Ba A Cikin Mafarki Ba Kawai. 

11

Tabbas Nasani Cewa Ban Kasance Farkoba Ban Kuma Zamo Karshan Furta Kalmar So Agarekiba Iyayen Ki Su Suka Fara. Amma Kuwa Zuciya Da Marari Ba’a Hanata Abinda Take Kauna Wanda Koda An Haneta Hakurinta Bai Wuce Kaddaraba. Har A Kullum Bakina Ya Saba Furta Kalmar So Agareki Wanda Ban Taba Canza Batuna Akan Hakan Domin Baiyanarki Ta Kasance Tamkar Fitowar Hasken Rana A Kowanne Lokaci Wanda Ganina Baya Samuwa Sai Dashi Hakan Yasa Nake Kallanki A Matsayin Jagora Wacce Zuciya Ta Kasance Mai Yin Alfahari Sannan Ta Amintarwa Kanta Zabi Mafi Dacewa Agareta.

12

Aminchin Allah Ya Qaratabbata Agareka Ya Kai Ma.Abocinrayuwata.Kaxamto Wata Nikuma Naxamto Xara Muhadu Mubada Haske.Kaxam To Ni Inxamto Kai Muhadu Mubawa Maqiya Kunya.Kaxamto Nono Inxamto Dambu Muhadu Muhana Maqiyammusha. Ina Sonka Xan Aureka Matuqar Inaraye Da Ixinin Allah Idam Harhaka Ta Faru To Lallai Xakasha Madararso Xallar Na Soyayya Basurki. Idan Na Aureka Xakasha Mamaki Insha Allah Kai Dai Muyi Fatan Allah Yakai Mu Lokacin.

13

Har A Kullum Bakina Ya Saba Furta Kalmar So Agareki Wanda Ban Taba Canza Batuna Akan Hakan Domin Baiyanarki Ta Kasance Tamkar Fitowar Hasken Rana A Kowanne Lokaci Wanda Ganina Baya Samuwa Sai Dashi Hakan Yasa Nake Kallanki A Matsayin Jagora Wacce Zuciya Ta Kasance Mai Yin Alfahari Sannan Ta Amintarwa Kanta Zabi Mafi Dacewa Agareta.Lokachi NE Ya Sanyoki Cikin Rayuwata Batareda Ni Dake Mun Taba Tsammanin Faruwar Hakan Ba,Yau Da Gobe Kuma Ta Baiwa Soyayyarki Damar Samun Sassaukar Doguwar Hanya Wadda Ke Zuwa Har Cikin Fadar Zuciya A Dan Karamin Lokachi,Ni Kuma Na Soki Fiyeda Duk Wani SO Danayi A Shekarun Baya,Wadannan Sune Dalilan Da Suka Sa Kikayi Zarra A Wajena,Me Xai Hana Zucia Tunowa Dake A Duk Lokacin Da Aka Ambaci Sunanki Koda Bake Ake Nufi Ba,Idan Har Mutumin Dake Dauke Da Kudi A Aljihunsa Zai Tuna Dasu Duk Bayan Yan Sakanni,Ni Me Zai Hana In Tuno Dake A Matsayinki Na Wadda Tsallake Aljihu Na Sakata A ZUCIA, Kuma I Love You.

14

Duk Da Ya Kasance Nida Ke Muna Nesa Da Juna Hakan Baya Hanani Tunaninki Hakan Baya Hanani Kaunarki Kin Zamo Ta Musamman Daga Cikin Mutane Na Musamman Da Na Ta6a Haduwa Da Su A Rayuwata, Kin Shiga Zuciyata Kin Zauna Ta Yadda Ba Zan Iya Mantawa Da Ke Ba Har Abada. Ina Fata Da Burin Kasancewarmu Tare A Daula Mafi Tsari Da Kyawun Burgewa Wato Aljanna. Cikin Nishadi Da Yalwatuwar Murmushin Fuska Nake Mai Furta Miki Cewa Ko Mutuwa Ta Rabamu Zamu Hadu A Aljanna Insha Allahu.

15

Zan Kula Dake Zan Baki Duk Wani Jin Dadi Da Mace Ke Nema Wurin Mijinta, Kuma Ina Fata Da Rokon Allah Yasa Na Iya Baki Duk Abunda Kike Bukata, Ina Sonki Sosai Fiye Da Dukkan Abunda Na Mallaka, Idan Banyi Rayuwata Dake Ba Bansan Yadda Zan Kasance Ba, Idan Ina Tina Ki Ji Nake Na Qagu Da Inga Na Mallakeki Na Ganki Cikin Inuwata Kiyi Frin Ciki Sanadiya Ta, Qaunar Nake Sosai

16

Haruffan Da Nayi Amfani Dasu Wajen Rubuto Maki Sakon Nan Ba Zasu Iya Nuna Maki Hoton Abinda Nake Son Sanar Dake Ba,Amma Zasu Kwatanta Maki Irin Yadda Abin Yake A Chikin Raina, ZUCIYATA Itace Babbar Igiyar Dake Juya Akalar Ruhina Da Gangar Jikina,SO DA KAUNA Yasa Nake Son In Zabeki Ki Zama Babbar Yar Majalisar Fadar Zuciya Wadda Zata Juya Akalata Da Zuciyar Tawa Gabadayanmu, Ni Kamar Maharbi NE Sakona Kuma Tamkar Kibiya CE A Hannuna Nayi Saitin Zuciyarki Irin Saitin Da Bani Tsammanin Zan Kuskure,Idan Har Ban Samu Ba Ina Fata Zaki Dubeni Da Idanun Tausayi Ki Qara Damke Soyayyata, I Love You

17

Bakina Yana Matukar Son Sanar Dake Irin Yadda Nake Sonki, Kunnena Kuma Yana Yana Jin Dadin Sauraren Sassanyan Sautin Siririyar Muryarki, Idona Kuma Kece Wadda Yafi Bukatar Gani A Kullum,INA SONKI Fiye Da Yadda Zan Jaraba Fasalta Maki Kuma Fiyeda Yadda Kema Zakiyi Hasashen Irin Girman Son,Ki Bani Dama In Zama Sashe Na Musamman Na Rayuwarki Mai Karfin Fada Aji A Cikin Fadar Zuciya,Har Wata Rana Siffar Fuskokinmu Ta Zama Kala Daya,Kada Kiji Tsoron Komai Game Dani Nayi Maki Alkawarin Soyayyata A Yanzu Da Muke Matsayin SAURAYI DA BUDURWA,Da Kuma Lokachin Da Zamu Zama MIJI DA MATA,Har Mu Koma TSOHO DA TSOHUWA, Zw Kushewar Mu. Kece Ki Kasance Uwargida A Gidana Na Duniya Da Kuma A Aljanna Musha Soyayya Muyi Rayuwar Da Ba Tinanin Mutuwa Ko Ciwon Ciki.

18

Na Za6eki Fiye Da Mallakar Komi Na Rayuwa Tamkar Shigar Lafiya Acikin Jikina. Na Nisanta A Cikin Sonki Da Kaunarki Ta Yadda Ba Mai Iya Hange Bare A Sami Kamata Domin Ni Agareki Na Kusantar Da Zuciyata. Na Kanyi Farin Ciki Da Abinda Soyayya Ta Samar Agareni Dadi Ko Wuya Musamman A Dangane Soyayyarki Badan Komiba Sai Dan Na Bayyana Sirrina Agareki Saboda Ke Ce Abin Da Rai Da Zuciya Suka Zamto Zabin Ta Domin Ki Zamo Abokiyar Rayuwar Ta. Ina Sonki Abune Wanda Baki Ya Saba Furtawa Akoda Yaushe Amma Nasarar Soyayyarki Gareni A Kullum Shine Ki Kasance A Matsayin Matar Aurena.

19

Zanso Ki Isarmin Da Wannan Sako Nawa Zuwa Ga Zuciyarki. Cikin Ko Wanne Lokaci Nakan Zamo Mai Nutsuwa A Duk Sanda Idanuwana Ke Tozali Ga Kyakkyawar Fuskarki. Ke Na Rika A Cikin Raina Da Sonki Nake Kwana Da Kaunarki Na Tashi. Sonki Halittane Dashi Nake Rayuwa A Jikina Dukkan Farin Cikin Zuciya Gareki Nake Samu. Ki Soni Domin Allah Kece Zabi Na Zuciyata Rayuwata Dake Ta Dace. 

20

Cikin Yan Kwanakin Nan Inajin Shauki A Zuciyata Yana Qaruwa Fiye Da Ko Yaushe. Soyayyar ki tana qaruwa Inajin Qaruwar kusancina Dake ta jini, Tabbas a jinina Nakejin Qaunarki. Inason Tsakanina Dake Mu Rinka Mutunta Junan mu. Mu Girmama Junan Mu. Mu Yiwa Junan Mu Duk Abunda Mukeso Kada Mu Sabawa Junan Mu. Idan Har Munason Qaunar Da mukewa Juna ta wanzu zuwa lokacin da muke Bukata To Sai Mun Girmama Soyayyar mu, har Yanxu na Kasa Yimiki Kishiya a Cikin Xuciyata Saboda Na Yarda Dake Sosai Fiye da Yadda kike Tsammani. Yadda Nakeji akanki Bana Iya Zayyanashi Kuma A jikina Nakeji yana Min Yawo. Ko Mutuwa Banason Ta Rabani Dake Wlh. Bakina ba zai Iya Furta Yadda zuciyata Take Jinki Ba. Kawai Hakuri Nake Na Danne, Kalamankine Kawai Suke Iya Min Magani.

Post a Comment

0 Comments