Game Da Wadanda Suka Samu Matsala Wajen Shiga Tsarin Bada Rance Na 'NYIF'

 Game Da Wadanda Suka Samu Matsala Wajen Shiga Tsarin Bada Rance Na 'NYIF'


Assalamu Alaikum WarahmatullahKwanakin baya matasa sun cike "Nigeria Youth Investment Fund" ko "NYIF", suka ce sun tura confirmation code zuwa email din mutane, amma hakika mutane da yawa basu ga sakon ba, ba'a tura musu ba, wanda ba'a tura masa ba, domin gyara wannan matsalar, sai ka/ki shiga website din kamar haka:


 https://nyif.nmfb.com.ng/


Ayi amfani da Ucbrowser ko kuma chrome wajen shiga sites din.


Da farko za ka/ki ga Options guda uku.


1. Apply Now. 

2. Loan Application.

3. Login.


Sai ka/ki shiga ka/ki danna wurin da aka rubuta "Login", idan ya bude za ka/ki ga ya kawo ma ka/ki wurin da za ka/ki saka Email din ka/ki, ko BVN din ka/ki, da kuma option na Password, toh kada ka/ki shiga wannan wurin.


Ka/ki je can kasa, za ka/ki ga wasu kananan rubutu guda uku.


1. Forgot password.

2. Register.

3. Did not get verification Token.


Sai ka/ki shiga wurin da aka rubuta "Did not get verification Token".

Sai ka/ki danna wurin, ka/ki saka email din ka/ki da ka/ki yi rijistan NYIF din dashi, sai ka/ki danna submit, zasu ce maka successfully.


Sai ka/ki jira na wasu awanni zasu tura ma ka/ki da confirmation code ko Link din ta email.

Idan sun tura sai ka/ki shiga email din ka/ki  danna, ka karashe har zuwa inda suke bukata.

Post a Comment

0 Comments