Ki Kula Dani Masoyiyata

 Yadda ake kula da masoyi koh masoyiya


Abunda Zuciya Take So, shine Qafa Yake Bibiya, Zuciyata Ke ta Hango Qafafuna Ke Suka Biyo, Saboda Irin Tarbar da Kika Min Dakuma Irin Kulawa Da Kike bani Yake sa Naji Tamkar ni Dake Mata Da Miji Ne. Kece Rayuwata, Kece Farin cikina, Kece Silar Dariyata, Idan Nayi Fishi Kece Mai Sani Murmushi, Idan Nayi Kuka Kece Me Sani Dariya. Amanar Zuciyata Yana Hanunki Idan Kika so Ki Rikeshi, Idan Kika so Ki Jefar, Amma Ki Sani Idan Babu Ke, Ni Bazan Yi Rayuwa Ba. Idan Kika Jefar Da Soyayyar da nake miki, To Kamar Kina Kunna Wutar yaki ne a cikin Qoqon Zuciyata, Farin ciki Zai Qaurace, Zaman Lafiya Ya Qare Daga Ranar, Firgici, Dimauta, Razani, Bakin ciki, Faduwar Gaba, Mafarki Maras Dadi Sune Abokan Tarayyar Zuciyata. Ina Qaunarki ne Daga Qoqon Raina. Ki Kula Dani Masoyiyata.

Post a Comment

0 Comments