Yadda ake fara soyayya da budurwa

Yadda ake fara soyayya da budurwa 

Kalaman da zaka fara gayawa budurwa idan kun hadu saboda ta soka dagaske kuma ka sace zuciyarta Nazo Gareki Tare Da Marmarin Zaki Dubeni da Zuciya Irin Taki Fara Mai Farin Hali, Ina Miko Miki Kalma irin Ta So, Domin Dacewarki Da Ita. Duba Ga Irin Yadda Kike Gidanar Da Rayuwarki Cikin Tsari Mai Kyau, Kin Iya Magana A Nitse, Bakya Fada Da Kowa, Kin Iya Murmushi, Maganarki Mai Zaki, Kinada Kamala, Araina Nake Jin Zaki Iya Soyayya, Domin Kinada Ilimi, Hankali, Tarbiya Irin Ta Iyaye, A cikin Zuciya Har Wani Tafasa Take idan Na Kalli Tafiyarki, Jikina Bari Yake Yayi dana Ke sauraron Muryarki. Idan Na Jima Ina Kallon Ki Mantawa Nake Da Kowace Mace a Rayuwa Ta Ke Kawai Nake Kallo Da Gani. Idan Kika Amince Da Soyayya Zan Saki Cikin Wata Aljannan Irin Ta Duniya Wacce Baki Taba Shiga Ba. Da Zan Samu Soyayyar ki Da Nafi Kowa Farin Ciki Domin Kece Silar Kasancewa Ta a Cikin Wannan Hali.


Inaso Na Fara Soyayya Dake, Amma Inajin Tsoro Ki Yaudareni. Inason Na Hada Inuwa Daya Dake, Kadewar Ganyen Bishiyarki Nake Tsoro. Ina Bukatar Jin Sanyi Mai Sanyaya Ruhi Irin Naki, Saidai Banason Kisa naji Zafi. Amma Ina Saka Rai Cewa Ke Ba Irin su Bace, Kina Da Tausayi Tare Da Kyakkawar Zuciya. 

Ku Cigaba Da Ziyartan Shafin Mu Domin Samun Garabasar Kalaman Soyayya www.Newlovevoice.com.ng 
Dannan domin shiga group dinmu 

Post a Comment

0 Comments