ABUBUWAN DA YAKAMATA KA SANI GAME DA MACE MAI KUNYA

ABUBUWA 10 DA ZAKA SANI AGAME DA MACE MAI KUNYA.

Furuci mai Daɗi ko mai kyau wanda zai fito daga bakin mace me kunya, ko Halayyar ta, ko Ɗabi'unta da kyan Halin ta suna da banbanci da sauran mata.

Yadda ake gane mace mai kunya

Related:

Idan har ka fahimci mace mai kunya kuma har ka aminta da ita, ka ƙulla alaƙa ta Soyayya da ita, to zaka samu farin ciki mai yawa.

Amma hakan ya dangana ne da irin yadda ka iya Mu'amalantar ta.


1. Soyayyar ta Maƙura Ce.

Idan har ka iya sace Soyayyar ta tana ɗaya daga cikin matan da sukewa namiji Soyayya mai zurfi. Soyayyar Mai tsafta ce kuma baya canjuwa ako wani time. Domin tana son masoyin ta ne da gabaɗaya zuciyarya. 

2. Tana da Biyayya

Mace ce wacce take tsayawa da masoyinta ako wani hali, da gaskiya da gaskatawa. Sannan Itace Abar yarda sannan tana da gaskiya.

3. Bata Nuna Soyayyar ta a fili.

Ɗaya ce daga cikin matan da suke maka makauniyar Soyayya amma a boye, Wacce bata da takura a Soyayya. Tana son kana bin rayuwa a hankali. Sannan Mace ce mai son sirri. Koda hira za kuyi ko Engagement kai harma Auren ku.

4. Bata son Namiji Me Kunya.

Bata son namiji mai kunya harma tafi son namijin da yake da yawan magana wanda baida kunya sosai wanda komai nasa ba irin nata bane. Zata Ƙaunace ka fiye da naka.

5. Zata Bada lokacin ta dakai.

Sukan ɗauki lokaci mai tsawo kafun su saba dakai, koda tana sonka bazata sake jiki dakai ba har sai bayan wani time mai tsawo. Domin ita ba irin sauran matan bane.

6. Bata da Son Kai!

Bata da Son Kai harma tana burin ta sadaukar maka duk abunda kake so koda ta fika son abun. Sannan suna da taimakon masoyin su. Sun iya abota sosai.

7. Bata da Saurin Fishi.

Saurin fishi ba halin mace mai kunya bane, duk irin yadda zaka bata mata rai ba kasafai zaka ga ta bata rai ba. Hasali ma idan tana sonka da gaske bazata taba ganin Baƙin ka ba.

8. Tana son Taga Mutane Suna Farin ciki.

Tana samun farin ciki da nishaɗi idan taga wasu mutane suna nishaɗi. Tama fi son tana daga nesa tana ganin abunda kuke itama tana dariya a boye.

9. Tafi Kowa Iya Fahimtar ka.

Mace mai kunya Zata fahimce ka sosai Fiye da sauran mutanen saboda ba wai kawai abunda kace take fahimta ba, tana iya gane abunda baka gane a tare da ita ba. Hanya mai sauƙin Koyo Shine Fahimta.

10. Ta Iya Murmushi

Idan har ka iya saka ta dariya to zaka mori Murmushin ta. Wannan Murmushin da zatayi tana yinshi ne daga cikin ƙasan Zuciyarta kuma na gaskiya ne. Sannan zaka fahimci kyawunta idan tana farin ciki.

Wannan Mace mai Kunya Kenan. 


Zaku iya shiga group namu na Telegram channel domin samun maka mantan wa ƴannan

Post a Comment

0 Comments